Ya kuke kallon salon mulkin Buhari da gwamnoni?
Ranar 29 ga watan Mayu shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da wasu gwamnonin kasar ke cika shekara daya a zangon mulkinsu su na biyu kuma na karshe. Shin kun gamsu da kamun ludayin gwamnatin Shugaba Buhari a shekarar farkon wa’adinsa na biyu? Wane gwamna kuke ganin ya ciri tuta? Yadda Buhari zai yi bikin cika shekara […]
Ranar 29 ga watan Mayu shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da wasu gwamnonin kasar ke cika shekara daya a zangon mulkinsu su na biyu kuma na karshe.
Shin kun gamsu da kamun ludayin gwamnatin Shugaba Buhari a shekarar farkon wa’adinsa na biyu?
Wane gwamna kuke ganin ya ciri tuta?
- Yadda Buhari zai yi bikin cika shekara biyar a mulki – Fadar Shugaban Kasa
- PDP ta yabi yadda Buhari ya tunkari ‘yan bindiga a Zamfara
- Gwamnoni za su gana da Malami kan ‘yancin bangaren shari’a da na majalisa
Daga cikin gwamnonin akwai wadanda a wannan ranar suke cika shekara daya a mulkinsu karo na farko.
Masu cika shekara daya su ne gwamnonin jihohin Legas da Ogun da Oyo a yankin Kudu maso yamma.
Sai gwamnan jihar Zamfara daga Arewa maso yamma da kuma jihohin Borno, Yobe, Adamawa da Gombe a Arewa maso Gabas.
Cikonsu shi ne gwamnan jihar Nasarawa a Arewa ta tsakiya.
Ku fada mana ra’ayinku
Shin kun gamsu da salon mulkin Shugaba Buhari a shakarar farkon wa’adinsa na biyu?
Wane gwamna kuke ganin ya ciri tuta?