Hoton awon ciki ya nuna tagwaye suna fada a cikin mahaifa
– Mahaifinsu ya yi mamakin ganin jariran da ba a haifa ba na fada da juna. – Akalla mutum miliyan 2.5 suka yi ta tafka muhawara a shafukan sada zumunta lokacin da aka yi ta yada hoton bidiyon awon ciki. – An haife su cikin koshin lafiya a asibiti Masu iya magana na cewa, […]
- – Mahaifinsu ya yi mamakin ganin jariran da ba a haifa ba na fada da juna.
- – Akalla mutum miliyan 2.5 suka yi ta tafka muhawara a shafukan sada zumunta lokacin da aka yi ta yada hoton bidiyon awon ciki.
- – An haife su cikin koshin lafiya a asibiti
Masu iya magana na cewa, yadda haihuwar tagwaye take kawo farin ciki biyu a lokaci guda. Haka kuma take zuwa da dawainiya.
Wani hoton awon ciki ya nuna ’yan tagwaye suna fada a yayin da suke cikin mahaifa. A wani faifan bidiyo da aka wallafa a kasar China an ga tagwayen suna shurin juna ta a cikin na’urar hoton awon cikin, yayin da ake yi wa mahaifiyar jariran awon cikin wata hudu.
Mahaifin tagwayen, Mista Tao, mai shekara 28, ya ce shi da kansa ne ya dauki faifan bidiyon a yayin da ya raka matarsa zuwa awon ciki a birnin Yinchuan a karshen bara.
Mista Tao, ya bayyana wa kafar labarai ta The paper cewa, abin ya burge shi matuka a yayin da ya ga jariran suna dambe a tsakaninsu.
Daga nan ne sai ya nadi bidiyon daga na’urar awon cikin, kafin daga bisani ya sanya shi a kan wata manhaja ta kafar labarai ta Douyin inda daga nan ne bidiyon ya yadu kamar wutar daji. Mista Tao ya ci gaba da cewa, bai taba tsammanin jariran biyu za su yi suna a shafukan yanar gizo ba tun kafin ma a haife su.
’Yan matan masu kiriniya an haife su cikin koshin lafiya sannan aka yi masu lakabi da sunan ’ya’yan itatuwan da mahaifiyarsu ta fi so, wato Çherry da Strawberry. Wannan bidiyo zuwa yanzu ya samu karbuwa daga masu ziyartar kafafen labarai har zuwa mutum miliyan 2.5 da kuma wadanda suka tofa albarkacin bakinsu a kansa har dubu 80.
Kafafen labarai da dama na kasar Chana irin su, China Daily sun yi ta yada wannan faifan. Wani mutum mai ban-dariya wanda ya kalli faifan, ya jefo barkwanci ta kafar Douyin inda ya ce; ‘Duk jaririyar da ta samu nasara (a fadan), ita ce babba a tsakaninsu idan an haife su.’
Wani kuma cewa ya yi; ‘Sun yi fada a cikin mahaifiyarsu, don haka idan an haife su za su so juna sosai.’
Mista Tao, ya kara bayanin cewa ya ga ’yan tagwayensa suna rungumar juna a wani sabon awon da aka yi a cikin watan Janairu.
“Mun damu ganin yadda jariran suka kasance ’yan kanana amma kuma sun damu da juna. Amma ina da yakinin za su zauna tare da juna cikin lumana idan suka girma,”Mista Tao, ya fada wa jaridar.
Kamar yadda mahaifinsu ya fada, tagwayen suna da wani sashe na jikinsu a manne da juna a lokacin suna cikin mahaifiyarsu wanda kuma yake da hadarin gaske wajen raba su. Amma cikin nasara an haife su cikin koshin lafiya.