Hoton budurwa mai sanye da tufafi mai ayoyin Alkur’ani ya harzuka Musulmin Saudiyya
Mutanen Saudiyya sun nuna fushinsu kan yadda wata budurwa, Balarabiya daga yammacin Isra’ila ta dinka rigar makaranta mai dauke da ayoyin Alkur’ani. An kuma baza hoton suturar tata a shafin sadarwa na facebookA shafin sadarwar Kwalejin Shenkar da ke koyar da Injiniyanci, an nuna yarinyar sanye da riga mai dauke da ayoyin Suratul Bakara. Sai […]
Mutanen Saudiyya sun nuna fushinsu kan yadda wata budurwa, Balarabiya daga yammacin Isra’ila ta dinka rigar makaranta mai dauke da ayoyin Alkur’ani. An kuma baza hoton suturar tata a shafin sadarwa na facebook
A shafin sadarwar Kwalejin Shenkar da ke koyar da Injiniyanci, an nuna yarinyar sanye da riga mai dauke da ayoyin Suratul Bakara. Sai dai wata kafar sadarwa ta kasar Isra’ila, ta yi nuni da cewa, wananan hoto saka shi aka yi a kan shafin facebook din kwalejin Shankar.
Iyaklan wadda ta zayyana fasalin dinkin, sun bayyana cewa ba manufarsu ba ce su aibatar Alkur’ani ko su harzuka Musulmi. Wannan aiki ne na makaranta, kamar yadda ak bayyana a shafin sadarwar Isra’ila.
Duk da kalaman lalama da aka bayyana shafin Isra’ila, Musulmi da dama sun harzuka, musamman a kasar Saudiyya. Sun kuma gargadi Musulmi su yi hattara da irin wadannan tufafi, domin makirci ne ake kulla wa Musulunci da Musulmi.