Hotuna: Ranar yara ta duniya
Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar Laraba 27 ga watan Mayu a matsayin Ranar Yara ta Duniya, domin a hadu a tuna da mahimmacin yara tare da kare hakkokinsu. Taken Ranar Yara ta bana shi ne yin tanadi ta hanyar inganta rayuwar yara, sai dai ba a samu damar yin bukukuwa kamar yadda aka saba […]
Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar Laraba 27 ga watan Mayu a matsayin Ranar Yara ta Duniya, domin a hadu a tuna da mahimmacin yara tare da kare hakkokinsu.
Taken Ranar Yara ta bana shi ne yin tanadi ta hanyar inganta rayuwar yara, sai dai ba a samu damar yin bukukuwa kamar yadda aka saba ba saboda cutar coronavirus, wacce ta hana yin tarurruka a duniya.
Domin tunawa da yara (manyan gobe), mun kawo maku wasu tsaffin hotunan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da wasu yara da ya gana da su a lokuta daban daban.