HOTUNA: Abba ya rantsar da sabon Sakataren Gwamnatin Kano

Naɗin sabon Sakataren Gwamnatin na zuwa ne bayan watanni biyu da sauke Baffa Bichi daga muƙamin.

HOTUNA: Abba ya rantsar da sabon Sakataren Gwamnatin Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rantsar da sabon Sakataren Gwamnatin Kano, Umar Farouk Ibrahim.

An dai rantsar da sabon Sakataren Gwamnatin ne a wani ƙwarya-ƙwaryan biki da aka gudanar ofishin gwamnan.

Aminiya ta ruwaito cewa, Kwamishinan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Kano, Barista Haruna Isa Dederi ne ya ba shi rantsuwar kama aikin.

Naɗin sabon Sakataren Gwamnatin na zuwa ne watanni biyu bayan sauke Dokta Abdullahi Baffa Bichi daga muƙamin da wasu kwamishinoni 5 da shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnan.

Wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan na Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ce an zaɓi sabon Sakataren Gwamnatin ne saboda ƙwarewar da ya ke da ita, wadda za ta taimaka wajen bunƙasa manufofin da gwamnatin ta Abba Kabir Yusuf ta sa a gaba.

NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Matan Arewa Karantar Ilimin Kimiyya?

HOTUNA: Abba ya rantsar da sabon Sakataren Gwamnatin Kano

’Yan bindiga sun kashe fasto a Gombe

An shiga nuna wa juna yatsa tsakanin Hamas da Isra’ila