Hotuna: An bude filin jirgin na Kano
An fara jigilar fasinjoji bayan bude filin jiragen sama na Malam Aminu Kano da ke jihar Kano a safiyar Asabar 11 ga Yuli, bayan kusan wata uku da rufe sufurin jirage na cikin gida a Najeriya. Annobar COVID-19 ce ta tilasta rufe bangaren wanda aka sake budewa a ranar 8 ga watan Yuli, da filayen […]
An fara jigilar fasinjoji bayan bude filin jiragen sama na Malam Aminu Kano da ke jihar Kano a safiyar Asabar 11 ga Yuli, bayan kusan wata uku da rufe sufurin jirage na cikin gida a Najeriya.
Annobar COVID-19 ce ta tilasta rufe bangaren wanda aka sake budewa a ranar 8 ga watan Yuli, da filayen jirage na Legas da Abuja, bayan sanya matakan kariya da kuma bayar da tazara a dukkanin matakai.
Ga wasu hotunan yadda harkoki suka fara gudana a filin jirgin: