Hotuna: An fara shirin bude masallatai a Legas

Shirye-shiryen bude masallatai da majami’u sun fara kankama a jihar Legas a daidai lokacin da ake ci gaba da yi wa wuraren ibadar rijiasta. Hakazalika an soma yi wa wuraren ibadar feshin magani duk a cikin shirin gwamnatin Legas na bude masallatan a ranar 19 ga watan Yuni, yayin da za a bude mujami’ai a […]

Hotuna: An fara shirin bude masallatai a Legas

‘Yan sa kai na feshin magani a harabar masallajin Alaja a Legas

Shirye-shiryen bude masallatai da majami’u sun fara kankama a jihar Legas a daidai lokacin da ake ci gaba da yi wa wuraren ibadar rijiasta.

Hakazalika an soma yi wa wuraren ibadar feshin magani duk a cikin shirin gwamnatin Legas na bude masallatan a ranar 19 ga watan Yuni, yayin da za a bude mujami’ai a ranar 21 ga wata Yuni.

Ga dai hotunan yadda aka yi feshin Masallacin Alhaja, wato babban masallacin juma’a na ‘yan Arewa mazauna Legas, masallacin da al’umar Arewa suka fara mallaka a Legas.

An yi wa masallacin feshin an kuma rushe rumfunan da ke kewaye da shi, wadanda a baya ‘yan kasuwa ke amfani da su wajen gudanar da cinikayya, duk a kokarin gwamnatin na rage cunkoso a daura da masallacin domin kare yaduwar annobar coronavirus.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara