HOTUNA: An kama mutane 6 masu yi wa ’yan ta’adda safarar kayan masarufi a Borno

Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da maganin kashe ƙwari, sinadarin acid, na’urar intanet ta Starlink, takin zamani, da buhunan shinkafa.

HOTUNA: An kama mutane 6 masu yi wa ’yan ta’adda safarar kayan masarufi a Borno

Sojojin rundunar Operation HAƊIN KAI sun kama wasu mutum shida da ake zargi da yi wa mayaƙan Boko Haram safarar kayayyakin masarufi a wani samamen da suka gudanar bayan tattara bayanan sirri a Jihar Borno.

Majiyoyin leƙen asiri sun ce samamen na zuwa ne bayan rahotannin da suka nuna cewa wasu masu haɗa kai da ’yan ta’addan na shirin kai musu sinadarai, magunguna da sauran kayayyakin masarufi.

A cewar majiyoyin, sojojin sun kafa shingen bincike a ranar 19 ga Yuli, inda suka kama waɗanda ake zargin suna tafe a cikin motoci biyar.

Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da kwalaye 202 na maganin kashe ƙwari, jarka ɗaya ta sinadarin acid, na’urar intanet ta Starlink, buhuna shida na takin zamani nau’in NPK, buhuna 10 na shinkafa, faratani 50 da fakiti 20 na famfunan feshi.

Majiyoyin sun ce ana zargin kayayyakin na cikin wani shiri ne na tallafa wa ayyukan ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas.

Tuni an miƙa waɗanda ake zargin tare da kayayyakin da aka ƙwato a hannun mahukunta domin ci gaba da bincike da gano sauran waɗanda ke da hannu a wannan aika-aikar.

Majiyoyin sojin sun ce kamen ya kawo wa ’yan ta’addan cikas a hanyoyin samar musu da kayayyaki, tare da jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da amfani da bayanan sirri wajen daƙile irin waɗannan ayyuka a yankin.