HOTUNA: An samu tsaikon fara zaɓen ƙananan hukumomi a Filato

An tsara gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin a ranar Laraba.

HOTUNA: An samu tsaikon fara zaɓen ƙananan hukumomi a Filato

Zaɓen ƙananan hukumomi da aka shirya gudanarwa a ranar Laraba a Jihar Filato, ya samu tsaiko sakamakon rashin zuwan jami’an Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar (PLASIEC), a kan lokaci.

Ana sa ran sama da mutane miliyan ɗaya ne za su zaɓi shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli a faɗin ƙananan hukumomin 17, a jam’iyyu 17 da za su fafata a zaɓen.

Wakilinmu ya ziyarci rumfunan zaɓe da dama a babban birnin jihar, ciki har da Tudun Wada, Anguwan Rukuba, Anguwan Rogo, Zinaria, da titin Bauchi, inda ya gano cewa har zuwa ƙarfe 11 na safe, ma’aikatan zaɓen ba su bayyana a wasu rumfuna ba.

A Jos ta Gabas, mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewar ba su ga jami’an zaɓe ko kayan zaɓe ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Kazalika, a Jos ta Kudu, tun ƙarfe 10:45 na safe mutane suka fara zaman jiran isowar jami’an zaɓe a rumfunan zaɓensu.

Wasu daga cikin masu kaɗa ƙuri’ar suna ta zirga-zirga tsakanin gidajensu da kuma rumfunan zaɓe.

Sai dai a wasu yankun jami’an zaɓen sun isa rumfunan zaɓe a makare.

 

Ga hotunan a ƙasa:

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya