HOTUNA: An soma kaɗa ƙuri’a a Zaɓen Ondo
Jam’iyyu 18 ne ke fafatawa a zaɓen, sai dai ana ganin takarar za ta fi zafi ne tsakanin APC da PDP.
A yau Asabar ne ake gudanar da zaɓen Gwamnan Jihar Ondo — ɗaya daga cikin jihohin Najeriya da ba a gudanar da zaɓukansu lokaci guda da na sauran jihohi.
Hukumar Zaɓe INEC ta ce mutum miliyan 2,053,061 ne suka yi rajistar zaɓe a faɗin jihar, yayin da matasa ke da kashi 35.41 cikin 100 na waɗanda suka yi rajistar zaɓen.
Tuni dai masu zaɓe sun fara kaɗa ƙuri’a kuma kawo yanzu yana gudana cikin kwanciyar hankali da lumana a wasu sassan jihar ciki har da birnin Akure.
Ana sa ran kammala kaɗa ƙuri’a da misalain ƙarfe 2:30 na rana, bayan duka mutanen da ke kan layin zaɓe a daidai wannan lokaci sun kammala jefa ƙuri’arsu.
Jam’iyyu 18 ne ke fafatawa a zaɓen, sai dai ana ganin takarar za ta fi zafi ne tsakanin gwaman jihar Lucky Aiyedatiwa na APC da Agboola Ajayi na PDP.