HOTUNA: An yi feshi a Babban Masallacin Agege

Mahukunta a Legas sun yi feshin maganin kashe kwayoyin cuta a Babban Masallacin Juma’a na Agege, wanda ake kira da Masallacin Alaja. A masallacin ne dai ake zargin wasu masallata sun yi wa jami’an Kwamitin Cika-Aiki kan Yaki da Coronavirus ihu sun kuma jefe su. Shugaban karamar hukumar Agege Alhaji Kola Egunjobi ne ya jagoranci […]

HOTUNA: An yi feshi a Babban Masallacin Agege

Masallacin Alaja a Agege, Legas na cikin manyan masallatan Juma’a da ke tara jama’a

Mahukunta a Legas sun yi feshin maganin kashe kwayoyin cuta a Babban Masallacin Juma’a na Agege, wanda ake kira da Masallacin Alaja.

A masallacin ne dai ake zargin wasu masallata sun yi wa jami’an Kwamitin Cika-Aiki kan Yaki da Coronavirus ihu sun kuma jefe su.

Shugaban karamar hukumar Agege Alhaji Kola Egunjobi ne ya jagoranci aikin feshin a ciki da harabar masallacin ranar Alhamis.

Bugu da kari ma’aikatan duba gari na jihar sun sanya shinge a kewayen masallacin wanda ke tsakiyar garin Agege.

Shugaban karamar hukumar Agege Alhaji Ganiyu Kola Egunjobi a lokacin da ya jagoranci feshin magani a Masallacin Alaja
Wasu daga cikin jami’an duba gari a lokacin da suke sanya shinge a Masallacin Alaja wanda mahukunta suka rufe
Masallacin Alaja, bayan da mahukunta a Legas suka sanya masa shinge biyo bayan harin da aka zargi wasu masallata da kai wa jami’an Kwamitin Yaki da Coronavirus a Legas
Jami’an duba gari a lokacin da suke killace Masallacin Alaja
Wani sashe na masallacin da mahukunta suka killace
Shugaban karamar hukumar Agege Alhaji Ganiyu Kola Egunjobi a lokacin da ya je feshi a wuraren da ke daura da masallacin
Daya daga cikin kofofin shiga Masallacin Alaja a lokacin da jami’ai ke yin feshin magani