HOTUNA: An yi jana’izar Dantata a Madina
Ba a taɓa samun wanda ya rasu a wata ƙasa daban ba sannan a kai shi Madina a binne shi sai a kan Aminu Dantata.
An yi jana’izar fitaccen attajirin ɗan kasuwar nan Alhaji Aminu Alhassan Dantata a birnin Madina na ƙasar Saudiyya.
Alhaji Aminu Dantata, wanda aka fi sani da Aminu Dogo, ya rasu ranar Asabar yana da shekara 94 a ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Lawabawa.
- Isra’ila na bincike kan harin dakarunta da ya kashe fararen hula a Gaza
- Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram 10 a Borno
Sai dai wani abin ban sha’awa shi ne yadda iyalansa suka yi ƙoƙarin tabbatar da burinsa da ma wasiyyarsa ta son a binne shi a Makabartar Baki’a, inda a nan ne ake binne sahabbai tun zaman Manzon Allah SAW – a birnin Madina (Garin Manzo) na Saudiyya a duk lokacin da ya bar duniya.
A bisa al’ada abin da aka sani shi ne za a binne ka a Madina ne kawai idan a can ka rasu. Amma a tarihin Nijeriya ba a taɓa samun wanda ya rasu a wata ƙasa daban ba sannan a kai shi Madina a binne shi sai a kan Aminu Dantata.





