HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja

An kawo gawar marigayi babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, zuwa Abuja a safiyar Alhamis, inda ake shirin gudanar da jana’izarsa a ranar Juma’a. Akwatin gawar Lagbaja, wanda aka lullube da tutar Najeriya, ya bar Legas tare da rakiyar manyan hafsoshin soji, kuma jirgin saman sojoji ya sauke gawarsa a filin […]

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja

An kawo gawar marigayi babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, zuwa Abuja a safiyar Alhamis, inda ake shirin gudanar da jana’izarsa a ranar Juma’a.

Akwatin gawar Lagbaja, wanda aka lullube da tutar Najeriya, ya bar Legas tare da rakiyar manyan hafsoshin soji, kuma jirgin saman sojoji ya sauke gawarsa a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe Abuja da misalin karfe 12:16 na rana.

Za a fara taron addu’o’in tuna marigayin daga yammacin Alhamis a filin paretin sojoji na shalkwatar da ke Mogadishu Cantonment, Abuja.

A ranar Juma’a da safe ne za a gudanar da babban taron jana’iza a Cibiyar Kiristoci ta Kasa (National Christian Centre) kafin a binne gawarsa a makabartar sojoji ta kasa da ke Abuja da yamma.

A makon da ya gabata ne gwamnatin Najeriya ta sanar da rasuwar Lagbaja a Legas bayan wata gajeruwar rashin lafiya.

Marigayin, wanda aka haifa a ranar 28 ga watan Fabrairu, 1968, ya rike mukamin babban hafsan sojin kasa na Najeriya tsawon shekara daya da wata hudu, tun bayan da aka nada shi a watan Yuni na 2023.

Lagbaja ya taka muhimmiyar rawa a wasu manyan ayyukan tsaro a fadin kasar, ciki har da Operation ZAKI a Jihar Benuwe, Lafiya Dole a Jihar Borno, Udoka a yankin kudu maso gabas, da kuma Operation Forest Sanity a jihohin Kaduna da Neja.

Marigayi Laftanar Janar Lagbaja ya fara aiki da rundunar sojin Najeriya tun bayan da ya shiga makarantar horar da sojoji ta NDA a shekarar 1987, inda aka nada shi Laftanar Soja a bangaren Infantry a shekarar 1992.

A tsawon aikinsa, ya shugabanci dakaru daban-daban, ciki har da gungun Bataliya ta 93 da 72 Special Forces Battalion.

Ya kasance cikakken ɗalibi a makarantar sojin kasar Amurka (U.S. Army War College), inda ya samu digirin digirgir a kan tsare-tsaren dabarun soja, wanda hakan ya kara masa kwarewa a harkokin jagoranci. Marigayin ya rasu ya bar mata, Mariya, da ’ya’ya biyu.

Akwatin gawar Lagbaja yayin sauka a filin Jirgin Saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja
Akwatin gawar Lagbaja
Akwatin gawar Lagbaja