Hotuna: Asari Dokubo ya ziyarci Ganduje a Abuja
Asari ya ziyarci Ganduje don taya murnar zama shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Dakubo da Ganduje
Tsogon Jagoran Tsagerun Neja Delta, Asari Dokubo, ya kai ziyarar taya murna ga shugaban jam’iyyar APC na Kasa, Abdullahi Umar Ganduje a Abuja.
Dokubo ya taya Ganduje murnar zama shugaban jam’iyya mai mulki ta kasa.
- Hannatu Musawa ta fadi gaskiya kan rashin kammala NYSC
- Nijar ta yanke wa ofishin jakadancin Faransa ruwa da wuta
A wani sako da ta wallafa a shafin X (Twitter), jam’iyyar mai mulki ta ce tsohon gwamnan Kano, ya karbi bakuncin dan gwagwarmayar a gidansa da ke babban birnin tarayya, Abuja.
“Shugaba Abdullahi Umar Ganduje, ya karbi bakuncin Tsohon Jagoran Masu Tayar da Kayar Baya a Neja Delta, Asari Dokubo, a wata ziyarar taya murna a gidansa da ke Abuja,” in ji jam’iyyar.
Ga hotunan ziyarar a kasa: