HOTUNA: Bala Mohammed ya gabatar da N465bn Kasafin Kuɗin Bauchi na 2025

Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya gabatar da N465,850,248,317 a matsayin Kasafin Kuɗin Jihar Bauchi na shekarar 2025. Gwamnan wanda ya yi wa kasafin laƙabi da Kasafin Kuɗin Ci gaba da Ayyukan Raya Ƙasa, ya gabatar da shi ga Majalisar Dokokin Bauchi a yau Alhamis domin tantancewa da kuma neman amincewarta. ’Yan bindiga sun sace mutum […]

HOTUNA: Bala Mohammed ya gabatar da N465bn Kasafin Kuɗin Bauchi na 2025

Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya gabatar da N465,850,248,317 a matsayin Kasafin Kuɗin Jihar Bauchi na shekarar 2025.

Gwamnan wanda ya yi wa kasafin laƙabi da Kasafin Kuɗin Ci gaba da Ayyukan Raya Ƙasa, ya gabatar da shi ga Majalisar Dokokin Bauchi a yau Alhamis domin tantancewa da kuma neman amincewarta.

Wakilinmu ya ruwaito cewa an yi kasafin ne da nufin magance ƙalubalen zamantakewa da tattalin arziki da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa a faɗin jihar.

Da yake gabatar da Kasafin Kuɗin, Gwamnan ya ce abubuwan da ke cikinsa sun yi daidai da yanayin halin da tattalin arzikin ƙasa da na duniya ke ciki a halin yanzu.

Gwamnan ya bayyana cewa kashi 39.3 wanda ya kai jimillar N182,743,955,931.60 na kasafin kudin an ware su ne domin ayyukan yau da kullum, yayin da kuma kashi 60.7 da shi ne jimillar N282,341,322,385.52 aka ware domin gudanar da manyan ayyuka.

Gwamna Bala ya ce ya ware wa ɓangaren gudanarwa N69,941,674,429.65  yayin da ɓangaren tattalin arziki ya samu N219,506,601,771.75, sai kuma jimillar  N9,538,142,748.76 da aka ware wa fannin shari’a.

Haka kuma, ya ce jimillar N166,098,829,366.96 aka ware domin inganta rayuwar jama’a wanda ya bayar da jimillar Kasafin Kuɗin gabaa ɗaya ya kama N465,085, 248, 317.12.

Gwamna Bala ya ce Kasafin Kuɗin na 2025 ya zarce na bara da kashi 18 cikin 100 domin samun damar aiwatar da biyan sabon tsarin fansho da na mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000.

Kazalika, ya ce gwamnati za ta tabbatar da kammala dukkan ayyukan da ake gudanarwa don buɗe tattalin arzikin jihar.

Sai dai ya ce hauhawar farashin da ke ƙara tsadar kayayyaki ya kuma shafi ayyuka da shirye-shiryen gwamnatinsa.

Shugaban Majalisar Dokoki na Jihar Bauchi Alhaji Abubakar Yakubu Suleiman ya yi alƙawarin cewa Majalisar za ta gaggauta yin bitar Kasafin Kuɗin domin amincewa da shi da zummar bai wa gwamnati damar ci gaba da ayyukan da take yi a faɗin jihar.

Ya yaba wa Gwamnan bisa gabatar da Kasafin kudin a kan lokaci da kuma muhimmanci da bayar wajen fifita manufofin da za su tasirantu a kan buƙatun al’umma.

Shugaban Majalisar ya ƙara da cewa, “Muna kira ga shugabannin ma’aikatu da hukumomi da ofisoshin gwamnati, da su zo su kare kasafin kuɗinsu, duk wanda ya ƙi zuwa ina tabbatar da cewa za a sanya masa takunkumi.”

A ƙarshe Shugaban Majalisar ya yaba da kyakkyawar alaƙar aiki da kr tsakanin ɓangaren zartaswa da na dokoki wanda ya ce hakan na ba da gudunmawa wajen zartar da ƙudirori da tsare-tsare masu amfanar jama’a kai tsaye.