HOTUNA: Barau ya bai wa ’yan sanda kyautar babura 1,000 a Kano

A shekarar da ta wuce Sanatan ya taɓa bai wa rundunar kyautar motocin aiki guda 22.

HOTUNA: Barau ya bai wa ’yan sanda kyautar babura 1,000 a Kano

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya bai wa Rundunar ’Yan Sandan Kano, kyautar babura guda 1,000.

Taron bayar da tallafin ya gudana ne a ranar Asabar a hedikwatar ’yan sandan da ke Bompai a Kano.

Ya bayar da tallafin ne domin taimaka wa jami’an ’yan sanda, wajen inganta ayyukansu da kuma tabbatar da tsaro a jihar.

Baburan waɗanda sabbi ne, kuma an ƙera su don yin aiki a kowane irin yanayi.

A shekarar 2023, Barau ya bai wa rundunar motocin aiki guda 22 domin tallafa wa ayyukanta.

Mahaifiyar Gwamnan Jigawa ta rasu

Najeriya ba ta cikin ƙasashen da suka fi cin bashi a Afirka – IMF

Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Babiana

An horar da mutum 500 dabarun adana ruwa don inganta muhalli a Gombe