HOTUNA: El-Rufai ya ziyarci Buhari a Daura

El-Rufai ya kai ziyarar ne kwana ɗaya bayan Atiku ya kai wa Buhari ziyara a Daura.

HOTUNA: El-Rufai ya ziyarci Buhari a Daura

Gidan Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari da ke Daura a Jihar Katsina, na ci gaba da ganin fuskokin manyan ’yan siyasar Najeriya.

Kafin yanzu, gidajen tsohon shugabannin ƙasa irin su Olusegun Obasanjo, Ibrahim Babangida da Abdulsalami Abubakar, ya kasance wajen kai ziyarar ’yan siyasa.

Sai dai a baya-bayan Daura na ci gaba da karɓar baƙi, inda tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya kai wa Buhari ziyara.

Idan ba a manta ba tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya kai wa Buhari ziyara a ranar Asabar.

Ya zuwa yanzu dai babu masaniya kan maƙasudin ziyarar da El-Rufai ya kai wa Buhari a Daura a ranar Lahadi.

Ga hotunan ziyarar a ƙasa:

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda