Duk da harin Isra’ila, Falasdinawa sun yi Sallar Idin a Masallacin Kudus

Luguden wutan Isra’ila bai hana Falasdinawa halartar Sallar Idi ba.

Duk da harin Isra’ila, Falasdinawa sun yi Sallar Idin a Masallacin Kudus

Dubban al’ummar Falasdinawa sun halarci Sallar Idi a Masallacin Kudus, a yayin da Isra’ila ke ci gaba da ke luguden bama-bamai a Zirin Gaza.

Daga cikin dare zuwa wayewar garin Alhamis, Isra’ila ta kai harin sama tare da luguden bama-bamai na sawon awanni a yankin zirin Gaza.

Falasdinawan sun halasci hawan idi a masallacin ne kasa da mako guda bayan an yi arangama tsakaninsu da jami’an tsaron Isra’ila da suka ritsa masu sallar Tahajjud a masallacin a cikin watan Ramadan.

Ga wasu hotunan sallar ta safiyar Alhamis:

Dubban Falasdinawa sun fito domin halartar Sallar Idi a Masallacin da ke Birnin Kudus. (Hoto: Ahmad Gharabli/AFP).
Cikin farin ciki da annuwar ranar Sallah, wani mahaifi na wa ‘yarsa wasa a wurin Sallar Idi.
Dandazon mahalarta Sallar Idin a harabar Masallacin Kudus, a safiyar Alhamis.
Wata Bafalasdiniya ta na daukar hoton Selfie a kusa da Masallacin Kudus. (Hoto: Ahmad Gharabli/AFP).
Matasan Falasdina a saman ginin Masallacin Kudus, suna daga tutocin Falasdinu da Saudiyya. (Hoto: AFP).