HOTUNA: Fashewar tankar gas ta kashe gomman mutane a Legas
A cikin ‘yan watannin nan, an samu fashewar tankokin mai dama a Nijeriya inda kusan mutum 300 suka rasu..

Wata tanka ɗauke da gas ta yi bindiga a Jihar Legas da ke kudu maso yammacin Nijeriya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar gomman mutane da jikkata da dama.
Lamarin ya faru ne a ranar Talata da dare a ƙarƙashin gadar mota ta Otedola, wadda tana daga cikin manyan hanyoyin da ke haɗe Legas da sauran sassan ƙasar.
- HOTUNA: An hana Gwamna Fubara shiga Majalisar Dokokin Ribas
- Ukraine ta amince da ƙudurin tsagaita wuta a fafatawarta da Rasha
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a lokacin da tankar ke ƙoƙarin juyawa domin kai gas ɗin wani gidan mai, inda a nan ne ta faɗi ta yi bindiga.
Mutane da dama da suka shaida lamarin sun ce ya ƙazanta, sakamakon yadda wuta ta kama motoci da dama da kuma gidaje da ke kusa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, a wani rahoto na wucin-gadi da ya fitar ya tabbatar da cewa lamarin ya rutsa da gidaje huɗu tare da haka kuma motoci 15 sun ƙone ƙurmus.
“Ana zargin hatsarin ya afku ne a lokacin da motar ke kokarin hawan hanyar Legas zuwa Ibadan ta gadar Otedola,” inji shi.
“Saboda haka, motar ta kife a kan hanya sannan ta yi bindiga nan take.”
“Har yanzu ana kididdige adadin rayukan mutanen da aka rasa, domin an gano gawawwaki biyu ne kawai.
“Lamarin ya kuma shafi wani asibiti mai zaman kansa, sai dai har yanzu babu cikakken bayani game da halin da waɗanda lamarin ya shafa a can.
“Za a ci gaba da bayar da rahoto a yayin da ake ci gaba da aikin ceto,” kamar yadda ya bayyana.
Jami’in Hukumar Agajin Gaggawa na Kasa (NEMA) shiyyar Kudu maso Yamma, Ibrahim Farinyole, ya tabbatar da faruwar lamarin da cewa suna ci gaba da ƙididdige asarar da aka yi.
A cewarsa, mutum daya ya mutu yayin da wasu hudu suka jikkata baya ga motoci 14 da shaguna hudu da suka ƙone ƙurmus.
A cikin ‘yan watannin nan, an samu fashewar tankokin mai dama a Nijeriya inda kusan mutum 300 suka rasu a ƙasar.