HOTUNA: Gobara ta laƙume shaguna 100 a Kasuwar Sakkwato

Wannan shi ne karo na uku cikin ƙasa da shekara ɗaya da ake samun tashin gobara a kasuwar.

HOTUNA: Gobara ta laƙume shaguna 100 a Kasuwar Sakkwato

Ana fargabar cewa wata gobara ta laƙume aƙalla shaguna 100 a Kasuwar Kara da ke Jihar Sakkwato.

Gobarar wadda ta tashi tun da Asubahin wannan Asabar ɗin ta shafe sa’o’i 9 tana ta’adi.

Wani ɗan kasuwar da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce tun da misalin ƙarfe 6:30 amma sai wurin ƙarfe 3:30 na rana aka samu nasarar kashe ta.

A cewarsa, gobarar ta yi ta’adi a ɓangaren shagunan masu sayar da abinci da suka haɗa da gero, dawa da masara da shinkafa.

Haka kuma, majiyar ta ce wutar ta yi ɓarna a ɓangaren masu ƙyamare da layin maƙera da masu maganin gargajiya.

“A ƙiyasi an yi asarar kuɗi za su kai Naira miliyan 500 domin dukkan shagunan da gobarar ta taɓa sun ƙone ƙurmus, masallaci ne kawai abun bai shafa ba.”

Ya buƙaci gwamnati da ta jingine batun siyasa a gefe wajen kafa kwamitocin da take ɗora wa alhakin bibiyar wannan ibtila’i domin ɗaukar matakan da suka dace bisa adalci.

Ya bayyana cewa wannan shi ne karo na uku cikin ƙasa da shekara ɗaya da ake samun tashin gobara a kasuwar.

Ya nanata kiran cewa bayan jajanta wa ’yan kasuwa akwai kuma buƙatar gwamnati ta ɗauki matakin kare dukiyar mutane daga irin wannan hasara.