Hotuna: Gobarar tankar mai a kan gada ta haddasa cunkoso na awanni a hanyar Legas
Gobara ta tashi bayan wata tankar mai ta gogi wata babbar motar dakon kaya ta kamfanin Dangote inda nan take suka kama da wuta, a kan gadar da ke babbar hanyar Legas zuwa Ibadan da tsakar dare. Hatsarin ya haddasa gagarumin cunkosu a hanyar wadda ta ita ake safarar daukacin kayayyakin masarufi daga gabar ruwa […]
Gobara ta tashi bayan wata tankar mai ta gogi wata babbar motar dakon kaya ta kamfanin Dangote inda nan take suka kama da wuta, a kan gadar da ke babbar hanyar Legas zuwa Ibadan da tsakar dare.
Hatsarin ya haddasa gagarumin cunkosu a hanyar wadda ta ita ake safarar daukacin kayayyakin masarufi daga gabar ruwa a Legas zuwa sassan Najeriya, kuma ita ce kadai mahadar Legas da sassan Najeriya.
Zuwa lokacin hada wannan rahoto ‘yan kwana-kwana da sauran jami’an kare hadura na kokarin kashe wutar wadda ta yi sama da awa bakwai tana ci, ko da yake ba a samu asarar rai ba. Wani shaida ya tabbatar wa Aminiya cewa ‘yan kwana-kwana sun yi kokari ta yadda wutar tankar ta tsaya ga manyan motocin biyu.
“Akwai karin wata motar tanka dauke da mai da ba ta kama da wuta ba, ita ake ta kokarin zuba wa ruwa domin gudun kada wuta ya tashi a kanta”, inji shi.
Ko wace hanya za a bi don magance gobarar motocin mai?
Ga wasu hotunan abin da ke faruwa da Aminiya ta samo.