Hotuna: Gwamnonin da aka yi wa allurar rigakafin Coronavirus a Najeriya
A makon da ya shude ne aka yi wa Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Yemi Osinbajo allurar rigakafin cutar Coronavirus ta AstraZeneca wanda aka yada a gidajen talabijin na kasar da kewaye. Shugaban Kasar tare da mataimakinsa sun yi hakan ne domin kara wa al’ummar kasar karfin gwiwa da janyo hankulansu a kan muhimmancin karbar […]
A makon da ya shude ne aka yi wa Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Yemi Osinbajo allurar rigakafin cutar Coronavirus ta AstraZeneca wanda aka yada a gidajen talabijin na kasar da kewaye.
Shugaban Kasar tare da mataimakinsa sun yi hakan ne domin kara wa al’ummar kasar karfin gwiwa da janyo hankulansu a kan muhimmancin karbar rigakafin cutar da ta zamto annoba ga duniya baki daya.
- ’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda biyu a Bauchi
- Hotuna: Mijin Zahra Buhari ya mallaki Zaki domin kiwon gida
- An harbe masu satar mutane biyu a garin Abuja
Kazalika, yunkurin masu rike da madafan ikon kasar na zuwa ne domin kawar da shakku dangane da rade-radin da ke yaduwa a kan amincin rigakafin.
Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi, shi kadai ne gwamnan da ya fito karara ya nesanta kansa da rigakafin wanda a cewarsa mutanen jiharsa ba aladu ba ne da za a yi musu wata rigakafin da ba su yarda da ita ba ballantana ita kanta cutar.
Sai dai takwarorinsa da dama sun karbi rigakafin a bainar jama’a domin nuna amincinsu a kanta da kuma kara wa al’ummarsu kwarin gwiwa.
A kidayar da Aminiya ta gudanar, ta lura cewa a halin yanzu akalla gwamnonin jihohi 14 sun karbi rigakafin. Ga hotunansu: