HOTUNA: Har yanzu gobara na ci gaba da ci a Kasuwar Singa da ke Kano

Tun dai da yammacin jiya Asabar ce gobarar ta tashi a Gidan Glass da ke babbar kasuwar kayan masarufi a Birnin Dabo.

HOTUNA: Har yanzu gobara na ci gaba da ci a Kasuwar Singa da ke Kano

Har kawo yanzu dai gobarar nan da ta tashi a Kasuwar Singa da ke Jihar Kano na gaba da ci zuwa wayewar gari ranar Lahadi.

Tun dai da yammacin jiya Asabar ce gobarar ta tashi a Gidan Glass da ke babbar kasuwar kayan masarufi a Birnin Dabo.

Sai dai wakilinmu ya ruwaito cewa, jami’an Hukumar Kashe Gobara na ci gaba da ƙoƙarin daƙile yaɗuwar wutar zuwa wasu gine-gine da ke kasuwar.