HOTUNA: Hatsarin tirela ya yi ajalin mutum 4, shanu 15 da awaki 20 a Neja
Mutum 13 sun jikkata yayin da biyu suka mutu nan take.
Mutum huɗu sun riga mu gidan gaskiya yayin da wasu 13 suka jikkata a sanadiyyar wani mummunan hatsari da ya auku a hanyar Lapai zuwa Agaie da ke Jihar Neja.
Aminiya ta ruwaito cewa hatsarin ya rutsa da tireloli uku waɗanda suka yi karo da juna ’yar tazarar mitoci ƙalilan zuwa garin Agaie.
- Mai gari ya tsere bayan mazauna sun cinna wa gidansa wuta a Kano
- NCDC ta tsaurara matakan shige da fice a Nijeriya saboda fargabar Ebola
Wani mazaunin yankin, Baba Yakubu ya bayyana cewa ɗaya daga cikin tirelolin da lamarin ya shafa ta ɗauko lodin dabbobi da suka haɗa da shanu da awaki
Shi ma Darekta Janar na Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Abdullah Baba Arah, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa an miƙa waɗanda hatsarin ya rutsa da su zuwa Babban Asibitin Agaie domin samun kulawa.
Ya alaƙanta faruwar lamarin da saɓa wa ka’idar tuƙi a yayin da ɗaya daga cikin tirelolin ta yi ƙoƙarin ƙetare wadda ke gabanta ba bisa ka’ida ba.
Ya ce hatsarin ya yi ajalin mutum huɗu — biyu da suka mutu nan take, sai kuma wasu biyun da suka ce ga garinku nan bayan an miƙa su asibiti.
Kazalika, ya ce shanu kimanin 15 da fiye da awaki 20 sun mutu a dalikin hatsarin.