HOTUNA: Jana’izar mahaifiyar Sanata Baba Kaka Bashir Garbai

Imam Idaini, Shettima Mamman Saleh, ne  ya jagoranci sallar Jana’izar a Fadar Shehun Borno.

HOTUNA: Jana’izar mahaifiyar Sanata Baba Kaka Bashir Garbai
Ranar Talata aka gudanar da Sallar Jana’izar Hajja Zainab, mahaifiyar tsohon Sanatan Borno ta Tsakiya, Baba Kaka Bashir Garbai.
Imam Idaini, Shettima Mamman Saleh, ne  ya jagoranci sallar Jana’izar a Fadar Shehun Borno.
Hajja Zainab Abba Bashir ta rasu ne a ranar da safe, a wani asibiti da ke Maiduguri tana da shekaru 82, a bar ’ya’ya da jikoki da dama.
Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima da Gwamna Babagana Zulum da sarakuna da Ambasada Babagana Kingibe suna daga cikin mahalarta jana’izar.
Hakaliza, tsohon gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff, da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC, Ali Bukar Dalori, sun samu zuwa.
Sanata Mohammed Ali Ndume, da Ministan Noma Sen. Abubakar Kyari, da shugabannin majalisar dokokin jihar da sauransu sun halarci jana’izar.

Dalilin da ba zan bai wa Gwamnatin Tinubu shawara ba — Sarki Sanusi

Hamas da Isra’ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana