Hotuna • Created August 11, 2022 18:59
Hotuna jana’izar sojojin rundunar tsaron shugaban kasa da da ’yan bindiga suka kashe
Sojojin su hudu sun gamu da ajalinsu ne a bakin aiki a watan Yuli
A ranar Alhamis aka gudanar da jana’izar wasu sojojin rundunar tsaron shugaban kasa da da ’yan bindiga suka kashe.
Sojojin su hudu sun gamu da ajalinsu ne a bakin aiki watan Yuli, kafin daga bisani a gudanar da Jana’izarsu Makabatar Sojoji da ke Maitama a Abuja.
Ga wasu daga hotunan:
Manyan sojojin suna sarawa a matsayin bankwana na karshe da wadanda suka kwanta dama. (Hoto: Idowu Isamotu).
Lokacin da ake sanya daya daga cikin hafsoshin da suka rasu a makwancinsa. (Hoto: Idowu Isamotu).
Lokacin da sojoji suka dauko gawarwakin zuwa Makabartar Sojoji da ke Abuja. (Hoto: Idowu Isamotu).
Lokacin da ake gudanar da ibadar jana’iza a Cocin Sojoji na St. John da ke Abuja. (Hoto: Idowu Isamotu).
Yadda aka dauko gawarwakin gabanin zuwa da su makabarta. (Hoto: Idowu Isamotu).
Ana mika wa matar daya daga cikin mamatan tutar Najeriya bayan an sanya shi a makwancinsa. (Hoto: Idowu Isamotu).
Iyalan mamatan sun karbi tutar Najeriya da gaisuwar ta’aziyya daga rundunar soji game da wannan babban rashi da aka yi. (Hoto: Idowu Isamotu).
Limaman cocin soji suna jagorantar addu’o’i gabanin a sanya sojojin da suka kwanta dama a makwancinsu. (Hoto: Idowu Isamotu).
Gabin wucewa da gawarwakin zuwa makabarta. (Hoto: Idowu Isamotu).
Wani sashe na mahalarta ibadar bankwana da mamatan a coci gabanin zuwa makabarta. (Hoto: Idowu Isamotu).