HOTUNA: Jirgin Kasan Kaduna zuwa Abuja ya kauce hanya

Jami’an tsaro sun isa wurin da jirgin ya yi hatsari da ke tsakanin wasu duwatsu.

HOTUNA: Jirgin Kasan Kaduna zuwa Abuja ya kauce hanya

Yadda fasinjojin da jirgin ya dauko suka yi cirko-cirko

Rahotanni sun bayyana cewa wani jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja ya kauce hanya a safiyar wannan Lahadin.

Jirgin wanda ya baro Kaduna ya kauce hanya ne da misalin karfe 9:30 na safiya a daidai yankin Jere da ke Ƙaramar Hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna.

Bayanai sun ce wannan lamari dai ya katse hanzarin gomman fasinjojin da jirgin ya dauko.

Kawo yanzu dai ana ci gaba da kokarin gyara jirgin wanda kusan taragonsa guda uku suka sauka daga hanya.

Tuni dai jami’an tsaro da suka hada da sojoji da ’yan sanda suka isa wurin da jirgin ya yi hatsari da ke tsakanin wasu duwatsu.

Yadda taragon jirgin ya sauka daga hanya
Wani sashe na taragon jirgin da ya sauka daga hanya
Yadda fasinjojin jirgin suka yi cirko-cirko

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya