HOTUNA: Kwankwaso ya ba da tallafin N50m ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri
Za mu ci gaba da ruɓanya ƙoƙarin gwamnati na bayar da tallafi ga waɗanda abin ya shafa.
Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayar da tallafin naira miliyan 50 ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a birnin Maiduguri na Jihar Borno.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis.
- Gwamnatin Kano ta ayyana Litinin hutun Ranar Takutaha
- Kashim Shettima zai jagoranci tawagar Nijeriya a taron MDD
“A yau [Alhamis] na kai ziyara Maiduguri domin jajanta wa gwamnati da al’ummar Jihar Borno kan ibtila’in ambaliyar ruwa da aka samu daga Madatsar Ruwa ta Alau.
“Wannan ibtila’in ya janyo ɓarnar da ba za ta misaltu ba ga mutanen Maiduguri tare da sanya jefa jama’a masu yawa cikin raɗaɗin rasa matsuguni.
“A namu ɓangaren, za mu ci gaba da ruɓanya ƙoƙarin gwamnati da sauran manyan mutane wajen bayar da taimako ga waɗanda abin ya shafa.”
Hotunan Kwankwaso yayin ziyarar da ya Fadar Gwamnatin Borno