HOTUNA: Kwankwaso ya je dubiyar Sakataren Gwamnatin Kano Baffa Bichi

Tun bayan dawowarsa daga jinya har yanzu Baffa Bichi bai koma ofishinsa ba.

HOTUNA: Kwankwaso ya je dubiyar Sakataren Gwamnatin Kano Baffa Bichi

Madugun jam’iyyar NNPC na Kasa, Rabi’u Musa Kwankwaso a wannan Alhamis din ya je dubiyar Sakataren Gwamnatin Kano Dokta Abdullahi Baffa Bichi wanda ya dawo daga jinya a Saudiyya.

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar NNPP a Zaben 2023, ya ziyarci Sakataren Gwamnatin ne a gidansa da ke unguwar Tudun Yola a Karamar Hukumar Ungogo tare da Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam.

Ana iya tun cewa, tun a ranar 7 ga watan Disambar bara ne Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya umurci Shugaban Ma’aikata, Yusuf Musa da ya ci gaba da lura da al’amuran ofishin Sakataren Gwamnatin har zuwa lokacin da zai dawo daga jinyar da ya tafi a ƙetare.

Tsohon Gwamnan Kano, Rabi’u Kwankwaso yayin da yaje dubiyar Sakataren Gwamnatin Kano Baffa Bichi

Aminiya ta ruwaito cewa, Baffa Bichi ya dawo gida Najeriya ne a ranar 7 ga watan Janairu, amma har yanzu bai koma ofishinsa ba.

Kwankwaso a gidan Baffa Bichi

Osimhen ya maka ɗan jarida a kotu

Abba ya karrama fitattun Kanawa 35

Asibitin Malam Aminu Kano ya hana motoci masu baƙin gilas shiga harabarsa

Mahaifin ma’aikacin Aminiya ya rasu