HOTUNA: Malaman Najeriya sun tattauna da shugaban gwamnatin sojin Nijar

Malaman sun ce tattaunawar ta samu gagarumar nasara

HOTUNA: Malaman Najeriya sun tattauna da shugaban gwamnatin sojin Nijar

Malaman addinin Musulunci daga darikun Najeriya daban-daban sun samu ganawa da Shugaban mulkin soja na Jamhuriyar Nijar, Abdulrahmane Tchiani a Yamai, babban birnin kasar.

A tsakiyar makon nan ne dai malaman suka ziyarci Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, a fadarsa da ke Abuja, inda suka shaida masa kudurinsu na kokarin shiga tsakani domin warware dambarwar siyasar kasar ta Nijar.

Daga nan ne kuma suka bar Najeriya ranar Juma’a, inda a jiya kuma rahotanni suka tabbatar da cewa sun sami nasarar ganawa ido da ido da shugaban.

Da yake jawabi a wajen tattaunawar, daya daga cikin malaman, Sheikh Kabiru Gombe, ya ce lokacin da suke Najeriya, sun yi wa Tinubu cikakken bayani a kan hatsarin da yake tattare da fara yakin Nijar, inda ya nuna gamsuwarsa, sannan ya ce zai gayyaci wakilinsu ya yi wa sauran Shugabannin ECOWAS wannan jawabin.

A baya dai, dukkan wani yunkuri na tattaunawa tsakanin wakilcin kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) da shugaban mulkin sojin na Nijar ya ci tura.

Sai dai a wannan karon, malaman na nuna cewa akwai alamun haske a ganawar tasu da shi.

Daga cikin malaman da suka halarci zaman akwai shugaban kungiyar Izala na Najeriya (JIBWIS), Sheikh Abdullahi Bala Lau da Sakataren kungiya, Sheikh Kabiru Gombe da Shugaban darikar Kadiriyya na Afirka, Sheikh Karibullah Nasiru Kabara da wakilin Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wato Sheikh Ibrahim Dahiru Bauci.

Sauran sun hada da Shugaban Jami’ar Al’Istiqamah da ke Sumaila a Jihar Kano, Farfesa Salisu Shehu, da Farfesa Mansur Sakkwato da dai sauransu.

Ga wasu daga cikin hotunan ganawar malaman da shugaban a Nijar:

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja