HOTUNA: Masu naɗin Sarki sun isa Fadar Gwamnatin Kano

Daga yanzu zuwa kowane lokaci Gwamna Abba zai rattaba hannu kan dokar rushe masarautun Kano biyar.

HOTUNA: Masu naɗin Sarki sun isa Fadar Gwamnatin Kano

Majalisar da ke da alhakin naɗa sabon Sarki ta isa Fadar Gwamnatin Kano a Yammacin wannan Alhamis ɗin.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake dakon naɗa sabon Sarkin Dabo bayan Majalisar Dokokin Kano ta rushe dukkanin masarautun jihar guda biyar.

Aminiya ta ruwaito cewa, daga yanzu zuwa kowane lokaci, Gwamna Abba Kabir Yusuf zai rattaba hannu kan sabuwar dokar rushe masarautun jihar da Majalisar Dokokin ta zartar a yau Alhamis.

Tuni dai masu naɗin sabon Sarki ƙarƙashin jagorancin Madakin Kano, Yusuf Nabahani ta isa Fadar Gwamnatin Kano.

Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Kano, Shehu Sagagi ne ya tarbi tawagar masu naɗin Sarkin wadda ta ƙunshi har Makama Sarki Abdullahi.

Ga hotunan isowar masu naɗa sabon Sarki a Kano