HOTUNA: Mayaƙan Lakurawa sun kashe mutum 17 a Kebbi

Mataimakin Gwamnan ya kuma miƙa ta’aziyarsa ga iyalan mamatan tare da alƙawarin hukunta waɗanda suka yi wannan aika-aikar.

HOTUNA: Mayaƙan Lakurawa sun kashe mutum 17 a Kebbi

An yi jana’izar aƙalla wasu mutum 17 da ake fargabar mayaƙan sabuwar ƙungiyar ta’addan ta Lakurawa sun kashe a garin Mera da ke Ƙaramar Hukumar Augie a Jihar Kebbi.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, ’yan ta’addan wanda a bayan nan aka bayyana ɓullar su a jihohin Sakkwato da Kebbi da ke Arewacin Nijeriya sun yi wannan aika-aikar ce a ranar Juma’ar da ta gabata.

Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ’yan bindigar sun shiga garin Mera da misalin ƙarfe ɗaya na dare, inda suka yi awon gaba da shanun mutane da dama.

Sai dai ya ce a yayin da mutane suka yi ƙoƙarin ƙwato dabbobin ne mayaƙan suka buɗe musu wuta kan mai uwa da wabi, lamarin da ya yi ajalin mutum 17 da a yau Asabar aka yi musu jana’iza.

“Mun yi ba-ta-kashi da su ne mun jikkata wasu daga cikinsu, sai dai sun tafi da shanu da ’yan uwansu da suka samu rauni, haka mu ma wasunmu sun samu rauni kuma an kai su asibiti.”

Ya ce “garin ba ya fama da matsalar tsaro sai yanzu ne da waɗannan ‘yan bindigar suka shigo har suka tafi da shanunmu bayan sun kashe al’umma.”

Mataimakin Gwamnan Kebbi, Sanata Umar Abubakar Tafida da ya tabbatar da faruwar lamarin ya halarci jana’izar mamatan tare da Sarkin Argungu, Sama’ila Muhammad Mera.

Mataimakin Gwamnan ya kuma miƙa ta’aziyarsa ga iyalan mamatan tare da alƙawarin hukunta waɗanda suka yi wannan aika-aikar.

Ya ce gwamnatin jiha za ta yi aiki sosai da jami’an tsaro don tabbatar da irin haka ba zai sake faruwa ba.

Shi ma Sarkin Argungu ya nemi al’umma da su haɗa kansu musamman miƙa bayanan duk wani abin da ba a gamsu da shi ba wajen jami’an tsaro don a tabbatar da an kare jama’a.

Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taro a Saudiyya

Zaɓen Ondo: Atiku ya gargaɗi INEC kan tafka maguɗin zaɓe

Sojoji sun tafka ƙazamin artabu da Bello Turji a Sakkwato 

Mutum 10 sun rasu a hatsarin mota a Jigawa