HOTUNA: NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye a cikin carbi da takalma

An cafke ababen zargin ne yayin da suke ƙoƙarin safarar hodar iblis ɗin zuwa ƙasa mai tsarki.

HOTUNA: NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye a cikin carbi da takalma

Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta NDLEA sun cafke wasu mutane da hodar iblis da suka ɓoye a cikin carbi da kuma takalma.

A cewar hukumar, an cafke ababen zargin ne yayin da suke ƙoƙarin safarar hodar iblis ɗin zuwa ƙasa mai tsarki.

Femi Babafemi, darektan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na NDLEA ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa tare da hotunan hodar iblis ɗin da aka kama.