HOTUNA: Obasanjo ya ziyarci Kwankwaso a Kano
Obasanjo ya samu tarba daga Kwankwaso tare da ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar NDC, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo.
Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya kai ziyarar girmamawa ga ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a gidansa da ke Kano a daren ranar Alhamis.
Obasanjo, wanda ke Kano domin wata ziyarar aiki, ya samu tarba daga Kwankwaso tare da ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar NDC, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo.

Mai taimaka wa Kwankwaso kan harkokin yaɗa labarai, Saifullahi Hassan, ya tabbatar da ziyarar a cikin wata sanarwa.
Ya bayyana cewa ziyarar ta bai wa shugabannin biyu damar yin tattaunawa cikin yanayi na mutunta juna da sada zumunci.

- ’Yan bindiga sun ƙone makaranta bayan sun karɓi harajin N10m a Neja
- Kachalla Fulani ya kashe mutum 7 bayan an janye sojoji a Matazu
- Zulum ya rufe sansanin ’yan gudun hijira mafi girma a Bama
Sai dai bai bayyana cikakken bayani kan abubuwan da suka tattauna ba.

Kwankwaso ya taɓa riƙe muƙamin Ministan Tsaro a wa’adi na biyu na mulkin Obasanjo tsakanin shekarun 2003 zuwa 2007, kuma tun daga lokacin suke ci gaba da kyakkyawar alaƙa.
