HOTUNA: Sabon rikici ya barke tsakanin dakarun Iraqi
An fara zanga-zangar ce bayan Muqtada al-Sadr ya yi ritayar daga siyasa
Sabon fada ya barke tsakanin dakarun da ba sa ga-maciji da juna a kasar Iraqi, kwana daya bayan likitoci sun tabbatar da kisan mutum 30 a Bagadaza, babban birnin kasar.
Rikicin ya fara ne bayan wani babban jagorar ’yan Shi’a na kasar, Muqtada al-Sadr, ya sanar da cewa zai yi ritaya daga harkokin siyasar kasar a ranar Litinin.
- Ba lallai mu kara zaman tattaunawa da Gwamnatin Buhari ba – ASUU
- Za a shafe kwana 4 ana tafka ruwan sama a Kaduna da Bauchi – NiMet
Lamarin dai ya sa magoya bayansa sun fusata, inda suka fantsama titunan kasar suna zanga-zanga, sannan suka yi taho-mu-gama da jami’an tsaro.
Tuni dai gwamntin mulki sojin kasar ta sanar da sanya dokar ta-baci a kasar don mayar da martani ga rikicin da ya barke, a daidai lokacin da ma’aikatan lafiya ke cewa mutane da dama sun sami raunuka.
Gwamnatin Iraqi dai ta shiga tsaka mai wuya ne tun lokacin da jam’iyyar Muqtada ta lashe kujeru mafiya rinjaye a zaben ’yan majalisar kasar na watan Oktoban bara, amma ba ta sami rinjayen da za ta kafa gwamnati ita kadai ba.
Ga wasu daga cikin hotunan tarzomar:
Hotuna: Aljazeera