HOTUNA: Sojoji sun ceto mata da yara 360 da Boko Haram ta sace a Borno

Jarirai biyu sun rasu sakamakon mawuyacin yanayin da aka fuskanta yayin jigilar waɗanda aka ceto zuwa wuraren tsaro.

HOTUNA: Sojoji sun ceto mata da yara 360 da Boko Haram ta sace a Borno

Rundunar Sojin Najeriya da ke ƙarƙashin Operation Hadin Kai (OPHK) ta ce ta ceto mutum 360, galibinsu mata da yara, waɗanda mayaƙan Boko Haram suka sace a ƙauyen Ngoshe da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno.

Majiyoyin soji sun bayyana cewa an gudanar da aikin ceton ne a ranar 6 ga Yuni a yankunan da ke kusa da tsaunukan Mandara, sakamakon wani samame na musamman da aka kai kan sansanonin ’yan ta’addar.

A cewar majiyoyin, rundunar sojoji ta musamman ce ta fara kai hare-haren da suka haifar da ruɗani a sansanonin Boko Haram, lamarin da ya bai wa sojojin rundunar ta 26 damar ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

An ce mafi yawan waɗanda aka ceto mazauna Ngoshe ne da aka sace lokacin da mayaƙan Boko Haram suka kai hari yankin a ranar 3 ga Maris, 2026.

Sai dai aikin ceton ya gamu da wani abin takaici, bayan da jarirai biyu suka rasu sakamakon mawuyacin yanayin da aka fuskanta yayin jigilar waɗanda aka ceto zuwa wuraren tsaro.

Rundunar ta ce an yi wa dukkan waɗanda aka ceto gwajin lafiya bayan isowarsu, yayin da aka kwantar da waɗanda ke buƙatar kulawar gaggawa a Asibitin Gwoza domin ci gaba da jinyarsu.

Haka kuma an samar musu da abinci da ruwan sha kafin a mayar da su wuraren ajiya masu tsaro domin shirye-shiryen haɗa su da iyalansu da kuma miƙa su ga hukumomin da suka dace.

Majiyoyin tsaro sun bayyana aikin a matsayin wata babbar nasara a ƙoƙarin da ake yi na ceto fararen hula da kuma tarwatsa hanyoyin ayyukan ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas.

Da yake yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin, muƙaddashin kakakin rundunar OPHK, Laftanar Kanar Haruna M. Sani, ya ce babban kwamandan rundunar, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, ya jinjina wa jarumta da ƙwarewar da sojojin suka nuna.

Ya ce nasarar ceton mutanen 360 ta nuna tasirin ingantaccen aikin leƙen asiri, haɗin gwiwar hukumomin tsaro da kuma ƙudirin sojojin Najeriya na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya ƙara da cewa rundunar za ta ci gaba da kai samame domin kawar da ragowar ’yan ta’adda, rushe hanyoyin tallafa musu da kuma hana sake faruwar irin waɗannan hare-hare a nan gaba.