HOTUNA: Ta’aziyyar Shugaban Sojin Kasa Bayan Harin Mauludi
Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja ya gana da al’ummar yankin Tudun Biri, inda harin kuskuren jirgin rundunarsa ya kashe mutum 85 a wurin Mauludi
Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar-Janar Taoreed Lagba ya kai ziyarar ta’aziyya kauyen Tudun Biri da ke Jihar Kaduna, domin jajanta wa al’ummar kan harin jirgin rundunar da ya kashe mutane 85 a taron bikin Mauludi.
Wasu mutane 66 sun jikka a sakamkon hare-haren bom guda biyu da jirgi mara matuki na rundunar ya kai wa taron Mauludin a daren Lahadi.
A lokacin ziyar ta’aziyyar Laftanar-Janar ya shaida wa al’ummar cewa ba bisa ganganci aka kai harin ba, tsautsayi ne, ya kuma yi addu’ar Rahamar Allah ta kai ga mamatan.
Ga yadda ziyarar ta kasance:
Babba Hafsan Sojin Kasan Najeriya, Taoreed Lagbaja, a lokacin ziyarar da ya kai a kauyen Tudun Biri bayan harin da jirgin rundunar ta kai wa masu halartar taron Mauludi. (Hoto: @HQNigerianArmy)
Al’ummar kauyen Tudun Biri, a lokacin da shugaban rundunar sojin kasa ya kai musu ziyarar ta’aziyya bayan jirgin rundunar ya kashe mutum 85 ya jikkata wasu 66 a kauyen. (Hoto: @HQNigerianArmy)
Zuwan shugaban rundunar sojin domin jajanta wa al’ummar Kauyen Tudun Biri kan harin kuskuren da jirgin rundunarsa ya kai wa mahalarta taron Mauludi. (Hoto: @HQNigerianArmy)
Kabarin mamatan harin kuskuren jirigin soji a yankin Tudun Biri da ke Jihar Kaduna.
Kabarin mutanen da harin kuskuren bom daga jirgin soji ya kashe a kauyen Tudun Biri a Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna. (Hoto: @HQNigerianArmy)
Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja da ‘yan rakiyarsa a lokacin ziyarar da ya kai bayan rasuwar mahalarta taron Mauludi da jirgin rundunar ya kai wa harin bom. (Hoto: @HQNigerianArmy)
Laftar-janar Lagbaja yana juyayin mutanen da harin kuskuren ya yi ajalinsu. (Hoto: @HQNigerianArmy)