HOTUNA: Taron kara haraji don hana shan sigari a Najeriya

Mahalarta taron sun kuduri aniyar aiki da gwamnati don hana yaduwar dabi’ar shan taba

HOTUNA: Taron kara haraji don hana shan sigari a Najeriya

An gudanar da wani taro kan illar shan sigari da kuma bukatar gwamnati ta kara harajin da take karba kan tabar, domin dakile yawan amfani da ita.

Kungiyar da ke sanya ido kan ayyukan majalisa (CISLAC) ce ta shirya taron tare da hadin gwiwar Ofishin Kula da Ma’aikata ta na Jihar Kano, ya kuma samu halartar wakilan hukumomin gwamnati da kuma kungiyoyi masu zaman kansu.

Masu halartar taron sun kudurci aniyar aiki da gwamnati don hana yaduwar dabi’ar shan taba a bisa tanadin dokar dakile shan taba ta kasa ta shekarar 2015.

Ga yadda taron ya gudana cikin hotuna:

Hatimin taron (Hoto: Balarabe Musa Mohammed)
Murtala Ali Jami’i mai walkiltar Shugaban CISLAC (Hoto: Balarabe Musa Mohammed)
Nasiru Mohammed Wakilin Shugaban Ma’aikata na Jihar Kano a taron (Hoto: Balarabe Musa Mohammed)
Ambasada Rabi Yusuf, Shugabar Kula da Hakkin Masu Bukata ta Musamman a taron (Hoto: Balarabe Musa Mohammed)
Mal. Khalid Musa Babban Maitaimakawa Gwamnan Kano kan harkokin Kannywood. (Hoto: Balarabe Musa Mohammed)
Daraktan Kula da Harajin Kayayyaki na Hukumar Tattara Haraji na Jihar Kano. (Hoto: Balarabe Musa Mohammed)
Nura Rabiu Daraktan Kula da Matasa na Ma’aikatar Cigban Matasa na Jihar Kano (Hoto: Balarabe Musa Mohammed).
Bilkisu Ado Zango, Shugabar Kungiyar Mata ‘Yan Jarida Reshen Jihar Kano (Hoto: Balarabe Musa Mohammed).
Abdullahi Zakari daga masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood. (Hoto: Balarabe Musa Mohammed).
Musa Kaila wakili daga kungiyar sa a taron (Hoto: Balarabe Musa Mohammed)
Mahalartar taron a lokacin tattaunawar (Hoto: Balarabe Musa Mohammed)
Solomon Adoga daya daga cikin jami’an CISLAC yana gabatar da jawabinsa a taron (Hoto: Balarabe Musa Mohammed).
Mahalarta taron banyan an gama (Hoto: Balarabe Musa Mohammed)