HOTUNA: Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Saliyo a Abuja

Nijeriya da Saliyo sun haɗa kai kan tsare-tsaren da suka shafi samar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba a Afirka.

HOTUNA: Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Saliyo a Abuja

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya gana da takwaransa na Saliyo Julius Maada Bio a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Ganawar tsakanin shugabannin ƙasashen Afirka biyu ta gudana ne a bayan labule, inda jami’an gwamnati kalilan ne suka halarta.

Shugaba Bio ya isa fadar shugaban ƙasa da misalin ƙarfe 12:30 na rana, kuma ya samu tarba daga Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila.

Haka kuma, shugaban na Saliyo ya samu tarba ta ban girma, inda rundunar sojojin shugaban ƙasa suka yi masa fareti tare da kade-kaden gargajiya.

Duk da cewa ba a san ajandar wannan ganawa ba, sai dai Aminiya ta samu cewa ba zai rasa nasaba yunƙurin inganta alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu ba.

Nijeriya da Saliyo mambobi ne na ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka da kuma ƙungiyar tarayyar Afrika, kuma sun haɗa kai kan tsare-tsaren da suka shafi samar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba a yankin.

Nijeriya ta taka rawar gani wajen ayyukan wanzar da zaman lafiya a ƙasashen Afirka da dama musamman Saliyo.