HOTUNA: Tinubu ya yi Sallar Idi a barikin Dodan da ke Legas

Ya yi sallar ce bayan dawo uwarsa daga Turai

HOTUNA: Tinubu ya yi Sallar Idi a barikin Dodan da ke Legas

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya gudanar da Sallar Idinsa a filin Idi da ke barikin sojoji na Dodanbda ke Jihar Legas a ranar Laraba.

Tinubu ya isa Legas ne ranar Talata bayan ya shafe mako daya a Turai, ya sami rakiyar iyalai, mukarrabai da abokansa.

Daga cikinsu akwai Shugaban Ma’aikatan Fadarsa, Femi Gbajabiamila, da dansa, Yinka Tinubu da Mai ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu da Mataimakin Gwamnan Legas, Babafemi Hamzat, da kuma tsohon Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola.

Ga wasu daga cikin hotunan sallar:

Abubuwan farin ciki da suka faru a 2024

Gyaran TCN ya janyo ɗaukewar wutar lantarki a Abuja

Babu sojojin ƙasar waje a yankinmu —Sakkwatawa

Yadda dagacinmu ya sassara ni da adda — Maraya