Manyan Labarai• Created July 29, 2020 12:20
HOTUNA: Yadda aikin Hajjin bana ke gudana
Kalli yadda aikin Hajjin 2020 ke gudan a Masallacin Harami cikin hotuna
Laraba 29 ga Yuli, 2020 ce ranar da mahajjata da ke sauke farali a kasar Saudiyya suke fara aikin Hajji.
Ana kiran makamanciyar ranar ta 8 ga watan Zhul Hijjah a kowace shekara ranar Tarwiyya.
Ga wasu hotunan yadda alhazan ke gudanar da ibadar a Masallacin Harami a Makkah kafin su wuce su kwana a Mina sannan su karasa zuwa filin Arfa a ranar Alhamis 9 ga Zhul Hijjah:
A wurin shiga Masallacin Harami, jami’an tsaro da sauran ma’aikata na lura da alhazai.An kawar da cunkoso, kowane alhaji na yin Dawafi ne yana bin kan layukan da aka zana a zagayen dakin Ka’abah.Kimanin mita biyu ne tsakanin mahajjaci da na gabansa a wurin Sa’ayi tsakanin Safah da Marwa.Alhazai sun bayar da tazara a cikin sahu suna ibada a Masallacin Harami.Yadda alhazai ke kai komo a wurin yin Sa’ayi cikin sahu uku a tsakanin Safah da Marah.Wani mahajjaci yana yin addu’a bayan kammala sallar nafilar bayan Dawafi