HOTUNA: Yadda aka gudanar da hawan Sallah a Ilorin

Hawan ya ƙayatar da masu kallo da dama.

HOTUNA: Yadda aka gudanar da hawan Sallah a Ilorin

Masarautar Ilọrin da ke Jihar Kwara, ta gudanar da bikin hawan babbar Sallah a jihar.

Mahaya dawakai da dama suka yi hawa ƙarƙashin jagorancin Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari.

Bikin mai kayatarwa ya ja hankalin manyan baƙi daga jihar da baƙi.

Tun da farko a wani taron manema labarai a fadar sarkin, shugaban kwamitin hawan sallah a masarautar Ilorin, Injiniya Suleiman Alapasanpa, ya ce hawan zai ƙayatar ta hanyar kafa tarihi.

Ga hotunan yadda hawan ya kasance: