HOTUNA: Yadda aka karrama Janar Murtala Muhammed a Abuja
An kashe marigayi Janar ne tare da wasu muƙarrabansa, a wani yunƙurin juyin mulki da bai yi nasara ba a Legas, ranar 13 ga Fabrairu, 1976.
Manyan mutane sun hallara a Abuja, a ranar Juma’a, domin tunawa da cika shekaru 50 da kisan tsohon Shugaban ƙasa, Janar Murtala Muhammed.
An kashe marigayi Janar ne tare da wasu muƙarrabansa, a wani yunƙurin juyin mulki da bai yi nasara ba a Legas, ranar 13 ga Fabrairu, 1976.
- Ranar Litinin Tinubu zai karɓi Gwamnan Kano zuwa APC
- Yadda Janar Murtala ya sauya Najeriya cikin kwanaki 200
Jami’an rundunar sojin Najeriya sun yi bikin karrama shi tare da wasu manyan baƙi.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Farfesa Ibrahim Gambari, fitaccen jami’in diflomasiyya kuma tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa lokacin mulkin marigayi Muhammadu Buhari.
Jakadan Angola a Najeriya, Jose Zau shi ma ya halarci taron.
Wakilin Daily Trust Onyekachukwu Obi wanda ya halarci taron ya ɗauki hotunan:




