HOTUNA: Yadda aka tsaurara tsaro kafin yanke hukuncin Kotun Koli kan Zaben Shugaban Kasa

Hotunan yadda aka tsaurara matakan tsaro a Kotun Koli da kewaye kafin ta yanke hukunci kan zaben shugaban kasa na 2023

HOTUNA: Yadda aka tsaurara tsaro kafin yanke hukuncin Kotun Koli kan Zaben Shugaban Kasa

An tsaurara matakan tsaro tare da tare hanyoyi gabanin zaman kotun koli, wadda a yau za ta yanke hukunci kan shari’ar ƙalubalantar nasarar Shugaba Tinubu a Zaben Shugaban Kasa na 2023.

Ga hotunan abubuwan da ke wakana daga wakilinmu, Onyekachukwu Obi.

Jami’an tsaro sun tare hanyoyin da ke kaiwa zuwa Kotun Kolin da ke Babban Birnin Tarayya Abuja.

Tuni jami’an kotun kolin suka fara aiki gabanin zaman wanda zai raba aya da tsakuwa tsakanin Tinubu manyan abokan hamayyarsa biyu, Atiku Abubakar da Peter Obi.

Atiku, ɗan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da kuma takwaransa na Jam’iyyar LP Peter Obi kowannensu ke neman a ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Titunan yankin sun kasance watan, babu motoci, lamarin da ya tilasta wa ma’aikata da sauran mutane takawa a kasa domin zuwa inda suka nufa.

Idan kotun ta soke nasarar Tinubu, zai zama mutum na farko da kotun ta kwace kujerar shugaban kasa a hannunsa a tarihin Najeriya na shekaru 63 da samun ’yanci.

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano

Matashi ya shiga hannu kan safarar tabar wiwi

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou