HOTUNA: Yadda aka yi Jana’izar Sarkin Gudi na Yobe bayan rasuwarsa a Abuja
Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni ya ranar Juma’a ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar wajen hakartar taron.
An yi jana’izar Marigayi Sarkin Gudi da ke Jihar Yobe, Alhaji Isa Bunuwa Madugu Ibn Khaji, ranar Juma’a a Abuja, inda ya rasu a wani asibiti bayan fama da jinya.
Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni ya ranar Juma’a ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar wajen hakartar taron.
Sanarwar da Mamman Mohammad daraktan yada labarai na gwamna Buni ya fitar ta ce, gwamnan da ke halartar wani taro a Abuja ya yanke ziyarar tasa domin halartar jana’izar marigayi Sarkin da kansa.
Gwamna Buni ya samu rakiyar Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Yobe, Alhaji Chiroma Buba Mashio, Sanata Ibrahim Mohammed Bomoi, Sanata Musa Mustapha, da ’yan Majalisar Wakilai.
Sauran sun haɗa da sakataren gwamnatin jihar, Baba Malam Wali, ’yan majalisar dokokin jihar, da kwamishinoni, masu ba da shawara na musamman, shugabannin kananan hukumomi, Sarakuna, Malamai, sauran jama’a.
- Yadda binciken zargin tallafa wa Boko Haram ke tafiyar hawainiya a Majalisa
- Jihar Sakkwato ta ciyo bashin N70.4bn domin inganta kiwon lafiya
Gwamnan ya yi addu’ar Allah Ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma yi kira ga al’umma da su tsaya tsayin daka, kuma su yafe wa juna.
Gwamna Buni ya bayyana rasuwar sarkin a matsayin babban rashi ga dangi, Masarautar Gudi, Jihar Yobe da kuma Najeriya baki xaya.