HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Sheikh Hassan Jingir a Jos

Malamin ya rasu ne bayan ya sha fama da rashin lafiya.

HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Sheikh Hassan Jingir a Jos

Dubban al’ummar Musulmi ne suka halarci jana’izar Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Izala na Ƙasa, Sheikh Hassan Jingir, a garin Jos.

An gudanar da sallar jana’izar ne a ranar Alhamis a unguwar Anguwan Rimi da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato.

A cewar sakataren yaɗa labaran JIBWIS, Ahmad Ashiru, Sheikh Jingir ya rasu yana da shekara 70.

Ya rasu a gidansa da ke Jos bayan fama da rashin lafiya.

Ya rasu ya bar mata biyu da yara sama da 40.

Ga hotunan yadda aka yi jana’izar: