HOTUNA: Yadda aka yi Jana’izar Wazirin Borno, Mustapha Mukhtar
Shugaba Tinubu ya bayyana juyayinsa bisa rasuwar Wazirin Borno, Mustapha Mukhtar, wanda ya riga mu Gidan Gaskiya a ranar Asasbar.
A ranar Asabar aka yi jana’izar Wazirin Borno, Yerima Mustapha Muktar, wanda Imam Idaini na Borno, Shettima Mamman Saleh ya jagoranta a Maiduguri.
Shugaba Tinubu ya yi juyayinsa rasuwar Wazirin Borno, a sakon taziyyarsa ga Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi, ya kuma roki Allah ya kisan sa ya ba wa iyalansa juriyar rashin.
Yerima Mustapha wanda ya zama Wazirin Borno a 2007, shi ne firaminista kuma babban mashawarcin Shehun Borno; ya rasu yana d shekaru 50, ya bar mahaifiyarsa da mata hudu da yaya, 19 da kuma ’yan uwansa.
Dubban jama’a sun halarci jana’izar Wazirin Borno, ciki har da Gwamnan Babagana Zulum da mataimakinsa Umar Usman Kadafur da Sanata Kaka Shehu Lawan da Ministan Noma Abubakar Kyari da sauran jami’an gwamnati.
Shehu Dikwa, Ibrahim Ibn Umar Ibrahim, da Shehun Bama, Umar Ibn Shehu Kyari, da Sarakin Damaturu Shehu Hashimi II El-Kanemi da kuma Sarkin Gazargamu, Tijjani Ibn Saleh Gaidam, na cikin mahalarta jana’izar.