HOTUNA: Yadda ambaliya ta raba mutane da muhallansu a Mokwa

Ambaliyar ta yi ajalin sama da mutum 100 tare da lalata dukiya mai tarin yawa.

HOTUNA: Yadda ambaliya ta raba mutane da muhallansu a Mokwa

Wasu daga cikin mazauna yankin Mokwa da ambaliyar ruwa ta lalata wa gidaje a Jihar Neja, yanzu na zaune a sansanin ’yan gudun hijira.

Ambaliyar, wadda ta kashe sama da mutum 100, ta jawo asarar dukiya da lalacewar gidaje da dama a yankin.

Aminiya ta kai ziyara sansanin a ranar Talata, inda ta ɗauki wasu hotuna da ke nuna halin da waɗanda abin ya shafa ke ciki da yadda suke rayuwa a sabon wajen da suka koma.

 

Ga hotunan a ƙasa: