HOTUNA: Yadda bikin Takutaha ya gudana a Kano

Musulmi da dama sun yi shiga ta ƙawa, inda suka dinga rera waƙoƙin yabon Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad SAW.

HOTUNA: Yadda bikin Takutaha ya gudana a Kano

Dubban al’ummar Musulmi a Jihar Kano, sun gudanar da bikin Takuhata, wanda aka saba yi a ranar 19 ga watan Rabi’ul Auwal (sati ɗaya daga 12 ga Watan Rabi’ul Auwal), don murnar ranar sunan Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (SAW).

Wasu daga cikin waɗanda suka yi bikin sun sanya fararen kaya, wasu kuma suka sanya wasu launukan kaya na daban.

Mutane sun yi wa manyan titunan jihar ƙawanya, inda suka dinga rera waƙoƙin yabon Annabi.

Aminiya ta ruwaito yadda aka gudanar da bikin Maulidin bana a faɗin ƙasar nan.

Ga hotunan yadda bikin Takutaha ya gudana a Kano:

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos