HOTUNA: Yadda Boko Haram ta lalata Kwalejin Kagara da ke Neja
Yanzu haka makarantar da daina aiki, domin ɗalibai sun daina zuwa.
Kwalejin Kagara da ke Jihar Neja, wadda ta yi fice wajen yaye ɗalibai masu hazaƙa, yanzu ta zama kufai, sakamakon hare-haren Boko Haram.
A shekarar 2021, Boko Haram ta kai hari makarantar ta sace aƙalla dalibai da malamai 27.
- 2027: Zan iya haƙura da takara in mara wa matashi mai jini a jika baya – Atiku
- Jiya na yi barci mai daɗi bayan na soke faretin samun ’yancin kai
Bayan haka kuma an sake kai hare-hare a yankin, lamarin da ya tsoratar da ɗalibai, tare da hana su komawa makaranta.
Yanzu makarantar ta daina aiki, inda aka mayar da ita sansanin soja.
Wakilin Aminiya, Abubakar Akote, ya ziyarci makarantar, inda ya ɗauki hotunan da ke nuna halin da makarantar ke ciki a yanzu.